Www.awaisuharuna.xtgem.comAwaisu
Maraba da zuwa wannan shafi mai Al-barka

Shafi Don Karuwar Musulmi
Daga Dan uwankuAwaisu Al-Arabee Fagge 2
•Menu•
☀ Home
[«»]Aqidojin Ahlussunnah (100)
[«»]Shi'ah da shi'anci (80)
[«»]Bangarorin Raddi (30)
[«»]Al'amuraan Yau da Kullum (50)
[«»]Rayuwar Musulmi (40)
[«»]Tambaya da Amsa (35)
[«»]Abubuwan Tarihi (75)
[«»]Da'awa Ta Zamani (70)
[«»]Karatu a MP3 (65)
[«»]Vidio (45)
[«»]About me(1)
Wannan shafin mallakarAwaisu Al-Arabee Fagge 3Ne
2025-04-19ZAMUJE QUDUS YAKI......
ZAMUJE QUDUS YAKI......
ZAMUJE QUDUS YAKI......

Hmm wannan wata kalma ce ta soki burutsu da muka sabaji daga bakin wasu makaryata tun muna yan yara.

Tunda mukayi wayo kukeci ana fada amma saide kash!!! Har yau bamuga an kama hanya ba.

Hasalima sai gani mukayi wasu sunje zaria amma sun mutu a hanya...
to ina kuma ace an tafi QUDUS????

Amma wannan duk bashi ne a gabanmu ba.

INA KUKE MASU BAKIN KAYA??????

Kuma ina ake mujahidan kasa mai tsarki suke mutsuttsuke wadanda yan uwan naku a kasar yemen???

Menene amfanin yawan da ake cewa kuna dashi???

Menene amfani kunshin da ake zuwa ana amsowa a Iran???

Ina kurinda ake fitowa kan titi ana buga kafafuwa ana kumfar baki???

Ina bugun kirjin da ake saka wasu bakaken karti makiya annabi SAW da yayan sa sukeyi???

Ko duk dama a iyaka arewaci ne kawai????

MTSWW!!!! Fa'arun, summa arun summa arun, shiqaqul mar'i in ajalidda'amu.

Dan Allah in an isa aje ayi maganin abin mana.

Karyar banza da hofi kawai!!!

"Fa'in lam taf'aluw, walan taf'alu"

Allah ya sauwake

Awaisu Al'arabee Fagge
6-4-2015

HABA AKRAMAKALLAH!!!!!!!
Ada malamai sunayin iyayakar kokarinsu wajen bayyana gaskiyar nassoshin ayoyin Allah kokuma hadisan manzon rahama SAW, kuma hakan ne yasanyawa malaman qima da daraja a idon dalibai, shugabanni, masu hannu da shuni kuma yake sakawa karantarwar tasu karbuwa.
Amma yanzu mun shigo wani hali da malaman mu bawai sunason doramu akan gaskiya bane, kawai fatansu shine sunemo abinda zaiyi dede da son zuciyarsu sai su bayyabawa mabiyansu, idan kuma basu sami wani nassi wanda zai goyi bayan dalilinsuba sai su nemo wani nassin wanda kwata-kwata ba bashida alaqa a dalilin da suke nema ba. Sai sudora mabiyansu akai kuma suhau kai suyi dare dare.
Akwanakin baya aka samu wani shehun malami aqasarnan wanda yakeso yakafa hujja da ayar qur'ani domin nuna cewa maulidi addini ne, toh da malamin yarasa huja sai yaje ya dauko wata aya datake cikin suratu yunus, kuma yayi mata karfa karfa da Karen tsaye kuma ya banqara ayar har yafassarata da son zuciyarsa kuma yace haka Allah yake nufi da ita. Wannan ayar itace:-
قُلْ بِفَضْلِ اللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَلِكَ فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِمَّا يَجْمَعُونَ
(yunus 58)
Ma'ana: Allah yace "kace musu da falalar Allah da rahamarsa ne yakamata mutane suyi murna suyi farin ciki, hakan shine mafi alkhairi fiyeda abun dasuke Tarawa.
Shikuma malamin sai yace " بِفَضْلِ اللَّهِ ai haihuwar annabi kenan, وَبِرَحْمَتِهِ kuma tana nufin da rahamarsa, فَلْيَفْرَحُوا sai yace kuyi maulidi, hakan shi yafi alkhari fiyeda abinda kuke Tarawa.
Wallahi lokacin da naji wannan tafsirin saida hankalina yatashi, saboda narantse da Allah nasan cewa shi kanshi lokacinda yake fassara ayar ahaka shima yasan karyane ba hakan Allah yake nufi ba. Dalili kuwa shine babu wani malami nada kona yanzu daya taba fassara ayar ahaka sai shi.
Naduba duk wani tafsiri dayake hannu na amma banga wanda aka rubuta makamanci abinda malamin yafada ba.
Irin wadannan ayoyim su ake cewa 'mutashabih' (wadanda ake iya dora musu wata ma'ana wadda ba tasu ta asaliba) wanda kuma duk wanda yakeda ilimin ulumul qur'an yasan ba'a kafa hujja da aya mutashabiha har sai idan ansamu aya muhkama da tagoyi bayan waccan, saboda Allah yace
فَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَاتَشَابَهَ مِنْه
(ali imran)
Ma'na: amma wadanda suke da cuta azuciyarsu, sune suke bin ayoyi mutashabihai.
Idan kaduba a haqiqanin gaskiya ai haihuwar manzonmu falalar Allah ce ga bayinsa kuma rahama ce, to amma matsalar shine haka Allah yake nufi da ayarsa????
Amsa; a'a, zan kawo tafsirin ayar acikin tafsirin farko a dunia (tafsirud-dabariy). Malan yace:
القول في تأويل قوله تعالى : { قُلْ بِفَضْلِ اللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَلِكَ فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِمَّا يَجْمَعُونَ (58) }
قال أبو جعفر: يقول تعالى ذكره لنبيه محمد صلى الله عليه وسلم:(قل) يا محمد لهؤلاء المكذِّبين بك وبما أنزل إليك من عند ربك= (1) (بفضل الله)، أيها الناس ، الذي تفضل به عليكم، وهو الإسلام، فبيَّنه لكم ، ودعاكم إليه =(وبرحمته)، التي رحمكم بها، فأنزلها إليكم، فعلَّمكم ما لم تكونوا تعلمون من كتابه، وبصَّركم بها معالم دينكم، وذلك القرآن =(فبذلك فليفرحوا هو خير مما يجمعون)، يقول: فإن الإسلام الذي دعاهم إليه ، والقرآن الذي أنزله
عليهم، خيرٌ مما يجمعون من حُطَام الدنيا وأموالها وكنوزها.
Toh bisa al'adar tafsirin malam yada da yawan kawo hadisai da sukazo domin fassara ayar da kafe Magana akanta. Toh zan kawokadan daga cikin hadisan,
- حدثني علي بن الحسن الأزدي قال ، حدثنا أبو معاوية، عن الحجاج، عن عطية، عن أبي سعيد الخدري في قوله:(قل بفضل الله وبرحمته فبذلك فليفرحوا) ، قال: بفضل الله القرآن(وبرحمته) أن جعَلَكم من أهله. (1)
17669- حدثني يحيى بن طلحة اليربوعي قال ، حدثنا فضيل، عن منصور، عن هلال بن يساف:(قل بفضل الله وبرحمته فبذلك فليفرحوا) ، قال: بالإسلام الذي هداكم، وبالقرآن الذي علّمكم.
17670- حدثنا أبو هشام الرفاعي قال ، حدثنا ابن يمان قال ، حدثنا سفيان، عن منصور، عن هلال بن يساف:(قل بفضل الله وبرحمته)، قال: بالإسلام والقرآن=(فبذلك فليفرحوا هو خير مما يجمعون)، من الذهب والفضَّة.
17671- حدثنا ابن بشار قال ، حدثنا عبد الرحمن قال ، حدثنا سفيان، عن منصور، عن هلال بن يساف، في قوله:(قل بفضل الله وبرحمته) ، قال: "فضل الله" ، الإسلام، و"رحمته"، القرآن.
17672- حدثني علي بن سهل قال ، حدثنا زيد قال ، حدثنا سفيان، عن منصور، عن هلال بن يساف، في قوله:(قل بفضل الله وبرحمته)، قال: الإسلام والقرآن.
Dukkan wadannan hadisai sun nuna cewa falalar Allah ana nufin qur'ani ita kuma rahamarsa tana nufin musulunci, amma shi tsoho yace wai haihuwar annabi., yanzu kuma zamu leqa tafsirin ibn kasir
shikuma muga me yace;
وقوله تعالى: { قُلْ بِفَضْلِ اللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَلِكَ
فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِمَّا يَجْمَعُونَ } (1) أي: بهذا الذي جاءهم من الله من الهدى ودين الحق (2) فليفرحوا، فإنه أولى ما يفرحون به، { هُوَ خَيْرٌ مِمَّا يَجْمَعُونَ } أي: من حطام الدنيا وما فيها من الزهرة الفانية الذاهبة لا محالة، كما قال ابن أبي حاتم، في تفسير هذه الآية: "وذُكِر عن بَقيَّة (3) -يعني ابن الوليد -عن صفوان بن عمرو، سمعت أيفع بن عبد الكلاعي يقول: لما قُدم خراجُ العراق إلى عمر، رضي الله عنه، خرج عُمَرُ ومولى له فجعل عمر يعد الإبل، فإذا هي (4) أكثر من ذلك، فجعل عمر يقول: الحمد لله تعالى، ويقول مولاه: هذا والله من فضل الله ورحمته. فقال عمر: كذبت. ليس هذا، هو الذي يقول الله تعالى: { قُلْ بِفَضْلِ اللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَلِكَ فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِمَّا يَجْمَعُونَ } وهذا مما يجمعون.
وقد (5) أسنده (6) الحافظ أبو القاسم الطبراني، فرواه عن أبي زُرْعَة الدمشقي، عن حَيوة بن شُرَيح، عن بقية، فذكره.
Shima nasan ba zaiyi wa duk wani mai zuwa makaranta wahalar fassarawa ba. Zan tafi zuwa tafsirin wanda yafi kowa iya tafsiri a dunia (abdullahi bn abbas) shikuma muji mai yace
قُلْ يا محمد لأصحابك { بِفَضْلِ الله } القرآن الذي أكرمكم به { وَبِرَحْمَتِهِ } الإسلام الذي وفقكم به { فَبِذَلِكَ } بالقرآن والإسلام { فَلْيَفْرَحُواْ هُوَ خَيْرٌ } يعني القرآن والإسلام { مِّمَّا يَجْمَعُونَ } مما يجمع اليهود والمشركون من الأموال
Shima wannan afili yace. Zan tsaya da kawo hujjoji haka ba don un kae ba, sai don na sauwakewa mai karatu yawan rubutu.
To abin tanbaya anan shine:
1: malam ya aikai fassararka tasha banban da ta dabari da ibn kasi da abdullahi bn Abbas???
2; ko kafisu iya fassara ne???
3; kokum a kafisu son annabi???
Wa;llahi yakamata m iji tsoron Allah a al'amuranmu.
Irin wadannan maganganunne idan mun fada sai ace wai bamuda kunya kuma alhali gaskiya ne. to indai wannan shine rashin kunya to kuwa bazamu dena ba. ya Allah kabamu ikon gane gaskiya kuma kabamu ikon binta kuma kabamu ikon gane karya kuma kabamu ikon guje mata.
A shirye naked a karbar gyaranku a duk inda kuke gani nayi kuskure.

Awaisu Haruna Fagge.


TAFSIRIN GASKIYA DAGA BAKIN ALHULBAYTI

Gabatarwa:
Bismillah wassalatu wassalamu ala rasulillah.

Wannan rubutun na kirkiro shi ne domin wadansu matsaloli danaga suna kunno kai cikin al'ummar musulmi. Musamman wadansu mutane masu kokarin raba tsakanin sahabbai da ahlulbaiti.
Shine nayi nufin dauko wasu ayoyi dasuke bayyana falalar sahabbai sanna nakawo fassarar da daya daga cikin ahlul baiti yayi mata.
Allah yamana muwafaqa amen.
Wanda zan dinga kawo fassarar tasa shine Abdullahi bn Abbas.
Na zabi na dinga kawo tafsirin ne daga fadar Abdullahi bn Abbas domin kasancewarsa wanda yafi kowa iya tafsiri a duniya gaba daya, sannan kuma domin kasancewarsa daya daga cikin ahlul bayti rasulullah.

AYA NA 1
Allah yace
فَأَمَّا مَنْ أَعْطَى وَاتَّقَى (5) وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَى (6) فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَى (7)
Ma'ana:- amma wanda yake bayarda dukiyarsa kuma yake jin tsoron Allah, * sannan kuma ya gaskakata kalmar shahada *toh da sannu zamu saukake masa yin ayyukan da'a.
Ga yadda Abudllahi bin Abbas ya fassara ayoyin

{ فَأَمَّا مَنْ أعطى } تصدق بماله في سبيل الله واشترى تسعة نفر من المؤمنين كانوا في أيدي الكافرين يعذبونهم على دينهم فاشتراهم منهم وأعتقهم { واتقى } الكفر والشرك والفواحش { وَصَدَّقَ بالحسنى } بعدة الله ويقال بالجنة بلا إله إلا الله { فَسَنُيَسِّرُهُ لليسرى } فسنهون عليه الطاعة ونستوقفه بالطاعة مرة بعد مرة ويقال الصدقة في سبيل الله مرة بعد مرة وهو أبو بكر الصديق
Ma'ana:- (فَأَمَّا مَنْ أعطى) ai wana yakeyi sadaka da dukiyarsa domin daukaka kalmar Allah kuma ya sayi muminai (bayi) guda tara da suke a hannun mushrikai suna azabtar dasu (saboda sunyi imani) ya siye su ya yanta su, (واتقى) yaji tsoron kafirci da shirka da alfasha, (وَصَدَّقَ بالحسنى) ya gaskata cewa akwai aljanna, ya gaskata kalmar shahada, (فَسَنُيَسِّرُهُ لليسرى) da sannu zamu sauwake masa yi mana da'a sannan zamu datar dashi da da'ar lokaci lokaci, wwasu sukace za'a sauwake masa cikayra dukiyarsa ga addini lokaci bayan lokaci, kuma wannan ayar tana magana ne akan sayyadina Abubakar radiyallahu anhu wa ani ssahabatu ajma'in.
Allahu akbar!!! Kunji bayanin gaskiya daga bakin Ahlulbaiti

AYA TA 2
Allah yace

لَقَدْ رَضِيَ اللَّهُ عَنِ الْمُؤْمِنِينَ إِذْ يُبَايِعُونَكَ تَحْتَ الشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمْ فَأَنْزَلَ السَّكِينَةَ عَلَيْهِمْ وَأَثَابَهُمْ فَتْحًا قَرِيبًا
Ma'ana:- hakika, tabbasa Allah ya yuarda da muminai wadanda sukayi maka mubaya'a a karkashin bishiya, sannan kuma Allah yasan abinda yake cikin zuciyarsu, sai ya saukarda nutsuwa a garesu sannan kuma tabbatarda budi zai same su bada dadewa ba.
Ga yadda Abdullahi bin Abbasa ya fassara ayar
{ لَّقَدْ رَضِيَ الله عَنِ المؤمنين إِذْ يُبَايِعُونَكَ تَحْتَ الشجرة } يوم الحديبية شجرة السمرة وكانوا نحو ألف وخمسمائة رجل بايعوا رسول الله صلى الله عليه وسلم بالفتح والنصرة وأن لا يفروا من الموت { فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمْ } من الصدق والوفاء { فَأنزَلَ } الله تعالى { السكينة } الطمأنينة { عَلَيْهِمْ } وأذهب عنهم الحمية { وَأَثَابَهُمْ } أي أعطاهم بعد ذلك { فَتْحاً قَرِيباً } يعني فتح خيبر سريعاً على أثر ذلك .
Ma'ana:- (لَّقَدْ رَضِيَ الله عَنِ المؤمنين إِذْ يُبَايِعُونَكَ تَحْتَ الشجرة) (hakika Allah ya yarda da muminai yayinda suke maka mubayi'a a karkashin bishiya) a ranar sulhun hudaibiyyah, a lokacin yawansu yakai mutum dubu daya da dari biyar, sunyiwa annabi mubaya'a akan zasu taimaka masa sannan kuma bazasu gudu ba saboda mutuwa, (فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمْ) kuma Allah yasan abinda yake zuciyarsu na gaskiya da cika alkawari, (فَأنزَلَ) sai Allah ya saukar da (السكينة) nutsuwa (عَلَيْهِمْ) a garesu sannan kumaya kore musu hamayya da rarrabuwa (وَأَثَابَهُمْ) bayan haka sai Allah ya basu (فَتْحاً قَرِيباً) budi (budde khaibara) a kusa kusa bayan faruwar wancan abin,
Tanbihi- acikin nn=an zamu samu cewa Allah ya yarda da sahabbai wadanda sukayi bai'atur-ridwan.
Wani zai iya cewa ai munafukai ne kokuma ai daga baya sun canja, sai ince maka karya ne saboda ai Allah yace yasan abibda yake cikin zuciyoyinsu. Ko kana tunanin Allah zai yarda da maha'inta ne? wannan bazai taba yiwuwa ba. kenan duk mutum mai adalci dole ya yarda da kirki da tsarkin sahabban manzon Allah sallallahu alaihi wasallam.

AYA TA 3
Allah yace

وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَآمَنُوا بِمَا نُزِّلَ عَلَى مُحَمَّدٍ وَهُوَ الْحَقُّ مِنْ رَبِّهِمْ كَفَّرَ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَأَصْلَحَ بَالَهُمْ
Ga yadda Abdullahi bin Abbas ya fassara ayar
{ والذين آمَنُواْ } بالله ومحمد والقرآن { وَعَمِلُواْ الصالحات } الطاعات فيما بينهم وبين ربهم وهم أصحاب محمد عليه الصلاة والسلام { وَآمَنُواْ بِمَا نُزِّلَ على مُحَمَّدٍ } بما نزل الله به جبريل على محمد عليه الصلاة والسلام { وَهُوَ الحق مِن رَّبِّهِمْ } يعني القرآن { كَفَّرَ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ } ذنوبهم بالجهاد { وَأَصْلَحَ بَالَهُمْ } حالهم وشأنهم ونياتهم وعملهم في الدنيا
Ma'ana:- (والذين آمَنُواْ) (wadanda sukayi imani) da Allah da manson Allah da alkur'ani, (وَعَمِلُواْ الصالحات) sukayi aiyukan da'a acikin abinda yake tsakaninsu da yan uwansu dakuma abinda yake tsakaninsu da Allah, wadannnan kuwa sune sahabbab manzon Allah sallallahu alaihi wasallam, (وَهُوَ الحق مِن رَّبِّهِمْ) sannan kuma sunyi imani cewa kur'ani daga wajen Allah madaukaki yake, (كَفَّرَ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ) Allah ya kankare musu zunubansu domin jihadin da sukayi (وَأَصْلَحَ بَالَهُمْ) sannna kuma Allah ya kyautata halayensu, sha'anoninsu, niiyyoyinsu, da ayyukansu a duniya.
Wadannan fa sune sahabban manzona.
Idan basu zamanto nagari ba toh waye zai zama nagari???

AYA TA 4
Allah yace

مِنَ الْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُوا مَا عَاهَدُوا اللَّهَ عَلَيْهِ فَمِنْهُمْ مَنْ قَضَى نَحْبَهُ وَمِنْهُمْ مَنْ يَنْتَظِرُ وَمَا بَدَّلُوا تَبْدِيلًا
Ga yadda ibn Abbas ya fassara ayar
{ مِّنَ المؤمنين رِجَالٌ صَدَقُواْ } وفوا { مَا عَاهَدُواْ الله عَلَيْهِ فَمِنْهُمْ مَّن قضى نَحْبَهُ } نذره ويقال قضى أجله وهو حمزة بن عبد المطلب عم النبي صلى الله عليه وسلم وأصحابه { وَمِنْهُمْ مَّن يَنتَظِرُ } الوفاء إلى الموت { وَمَا بَدَّلُواْ } غيروا العهد { تَبْدِيلاً } تغييراً
Ma'ana;- (مِّنَ المؤمنين رِجَالٌ صَدَقُواْ) (daga cikin muminai akwai wadansu mutane da) suka gaskata kuma suka cika (مَا عَاهَدُواْ الله عَلَيْهِ فَمِنْهُمْ مَّن قضى نَحْبَهُ) abinda suka daukarwa Allah alkawari, daga cikinsu (su muminai) akwai wanda suka cika bakancen su, wasu kuma sukace akwai wadadanda ajalinsu yazo, kamar su hamza bin Abdulmudallib ashi da makamantansa, (وَمِنْهُمْ مَّن يَنتَظِرُ) acikinsu kuma akwai wadanda suke dauke da niyyar cika alkawarin har izuwa mutuwarsu, (وَمَا بَدَّلُواْ) basu canja ba, ai basu canja alkawarinda sukayiwa Allah ba (وَمَا بَدَّلُواْ) matukar canjawa.
Lallai kun samu shaida maimkyau daga maaliccinku masanin gaibu.

AYA TA 5
Allah yace

وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنْصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
Ga yadda Abdullahi bin Abbas ya fassara ayar:-

{ والسابقون الأولون مِنَ المهاجرين والأنصار } بالإيمان الذين صلوا إلى قبلتين وشهدوا بدراً { والذين اتبعوهم بِإِحْسَانٍ } بأداء الفرائض واجتناب المعاصي إلى يوم القيامة { رَّضِيَ الله عَنْهُمْ } بإحسانهم { وَرَضُواْ عَنْهُ } بالثواب والكرامة { وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ } بساتين { تَجْرِي تَحْتَهَا } من تحت أشجارها ومساكنها { الأنهار } أنهار الماء والخمر والعسل واللبن { خَالِدِينَ فِيهَآ }
مقيمين في الجنة لا يموتون ولا يخرجون منها { أَبَداً ذلك } الرضوان والجنان { الفوز العظيم }
Ma'ana:- (والسابقون الأولون مِنَ المهاجرين والأنصار) wadanda sukayi rigaye da imani na farko farko daga cikin mutanen makka dana madina, sune wadanda sukayi sallah a alqibla guda (baitul maqdis da dakin ka'aba) kuma suka halarci yakin badar, (والذين اتبعوهم بِإِحْسَانٍ) da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa , ai da cika farillai da kauracewa sabo har izuwa ranar tashin kiyama (رَّضِيَ الله عَنْهُمْ) Allah ya yarda dasu saboda kyautatawarsu (وَرَضُواْ عَنْهُ) kuma suma sun hyarda dashi dacewa zai saka musu da lada dakuma girmamawa, (وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ) Allah ya tanadar musu aljannatai wadanda (تَجْرِي تَحْتَهَا) abubuwand suke a karkashin bishiyunsu da wajen zaman dake ciki shine (الأنهار) kogi na ruwa, giya da zuma, sannan kuma (خَالِدِينَ فِيهَآ) zasu dauwama acikinta bazasu mutu ba kuma bazasu taba fita daga cikinta ba(أَبَداً) har abada. (ذلك) wannan aljannar a aka shigar dasu dakuma yardar da Allah madaukaki yayi dasu (الفوز العظيم) rabautace mai girma.
Tanbihi- Allah da kansa uabada shaida akan cewa ya yarda dasu kuma suma sun yarda dashi. Kuma gashi Abdullahi bin Abbas yanuna mana cewa wannan ayar tana magana ne akan MUHAJIRUNA da ANSARU dakuma wadanda sukabiyo bayansu da kyautatawa. Kaga kenan idan kabiyo bayansu da zagi da cin mutunci kenan kai baka ciki.
Sannan kuma kai wanda kabiyo bayansu da kyautatawa kasani fa albarkacinsu kasamu har Allah yayi muku kudinn goro yace dukgaba daya ya yarda daku.

JAHILCI DA SON RAN MASU BAKIN UNIFORM

Yanzunnan nake ganin rubutu da duk wani mutum mai ilimi bazai yishi ba

Wanda yayi rubutun Shine

ABDULLAHI GAMBO KATSINA AR-RAFIDIY

Duk dayake dai naga yayi cin amana ta ilimi, domin bashi yayi rubutun ba, daya daga cikin Media watch dinsu suka rubuta shikuma sai ya kwafo.

Ga abinda yake cewa

ANA ZATON WUTA A MAQERA SAI GAYA TA TASHI AMASAQA........ !!!

Masu cewa yan Shi'a suna zagin Sahabbai? Toh sai ga asirin masu zagin sahabban nan na asali yana qara tonuwa.

Ko kunsan???
IBN TAIMIYYAH (L) YACI ZARAFIN IMAM ALI BIN ABU-TALIB (AS)?

Yazo acikin littafin Minhajus Sunnah na Ibn Taimiyyah inda yake cewa:- "Haqiqa Allah yasaukar da wannan ayar ne akan Aliyu..

"Ya ku masu imani kar ku kusanci sallah kuna acikin maye (giya) .......

ﻭﻗﺪ ﺃﻧﺰﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻓﻲ ﻋﻠﻰ ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻻﺗﻘﺮﺑﻮﺍ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺃﻧﺘﻢ ﺳﻜﺎﺭﻯ ﺣﺘﻰ ﺗﻌﻠﻤﻮﺍ ﻣﺎ ﺗﻘﻮﻟﻮﻥ ﻟﻤﺎﺻﻠﻰ ﻓﻘﺮﺍ ﻭﺧﻠﻄﻮ

Don qarin bayani kuwa? Sai aduba
منهاج السنه النبويه
لابن تيميه
الجزءالسابع
ص237

Nikuma Awaisu nace:

KARAMIN SANI KUKUMI

Mai wannan rubutun da kuke gani yayi shi domin cin zarafin wani malami, bawai malamin zan kare ba. Don ba aikunmu bane kare malamanmu.

Amma abinda yafada ne yakeso yakafa hujja dashi domin nuna cewa basuyi laifi ba don sun zagi sahabbai.

Wannan abinda malam IBN TAYMIYYAH yafada hakane, kuma hadisi ne ta tabbatar da hakan.

Amma don Aliyu yasha giya a wancan lokacin baiyi laifi ba, domin ai a lokacin Allah bai haramta ta ba.

Ga duk mutum mai ilimi yasan cewa an fara hana shan giya ne da hukunci na rashin kamata, sannan akazo hukunci hana sha idan za'azo sallah sannan kuma aka hana gaba daya.

Idan kayi abu kafin a hana shi ai bakayi laifi ba.

Ai ba shi kadai ba, hadisi ya tabbata cewa Sayyadi Uamr shima yana sha Amma daga baya Allah yahana kuma suka daina.

Ai shine da Allah yace "...... Fahal antum muntahun???". Ma'ana: shin kun hanu? (Daga shan giya)?

Sai sayyadi Umaru yace "intahaina.. Intahaina.." Ma'ana: mun hanu.. Mun hanu..

Ai duk mai ilimi yasan cewa ba rana daya aka saukarda dukkan hukunce hukuncen addini ba, daya bayan daya suke sauka.

Yanzu misali. Mahaifinka yanada mota, sai yake baka mukulli, kaikuma sai kake hawa motar, ai bakayi laifi ba, amma daga baya sai yace maka, kai! Ajiya nake baka mukulli ba cewa nayi ka dinga hawa ba. Kaga ai daga lokacin in kahau ai kayi laiffi.

Saboda haka aje ayi karatu kuma a gyara niyya.

Kuna iya bina ta face book


☀Labarai




•Home•


«Kuna iya bina ta face book»

«Ko ta shafin mu na Tsarabar sunnah»

«Ku ziyarci Shafin Basheer journalist sharfadi»





  • AWAISUL-ARABEE FAGGE
  • ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow




  • Insane