WA'AZIN IZALA TA JIHAR KANO
WA'AZIN JIHA NA JIBWIS KANO
Kamar yadda sanarwa ta gabata akan cewa Kungiyar Izala ta jihar Kano zata gudanarda wa'azinta na Jiha bisa munasabar BUDE SABON MASALLACI DA MAKARANTA, hakan ya tabbata, domin an gudanar da wa'azuzzuka masu matukar fa'ida ga al'umma sannan kuma anyi wa'azin cikin nasara.
Shugaban kungiyar na Jihar Kano, Dr Abdullahi Saleh Pakistan shine ya jagorancin yan majalisar zartarwar sa domin haduwa da dinbin Al'umma a Unguwar Mandawari dake cikin Garin Bagwai inda anan ne aka baje-kolin wa'azin.
Tun farkon zuwan Shugaban dakuma tawagar tasa, sun fara kai ziyara ne zuwa sabuwar makarantar da aka mallakawa kungiyar domin gani da ido dakuma sa albarka, kana daga baya aka dunguma aka taho masallacin inda aka fara wa'azi batare da jinkiri ba.
Matasa dakuma dattawan malamai sun gabatarda wa'azi mai ratsa jiki, kuma duka wa'azin ya maida hankali ne akan cin zarafinda wata jarida tayiwa fiyayyen halitta SAW, jerin malaman da sukayi wa'azin sune:-
1- Sheikh Nura Umar K/mata
2- Sheikh Anas Assalafiy Fagge
3- Sheikh Jamilu Abubakar
4- Sheikh Muhammad Ghali
5- DR Abdullahi Saleh Pakistan.
Duk dayake akwai malamai dayawa da suka halarta; amma saboda karancin lokaci yasa aka takaita a haka.
Taron yasamu halarta manyan baki kamar su:-
- mataimakin shugaban kungiya na Kano, Sheikh Ahmad Muhd Bichi
- Daraktan yada labarai na kungiya na Kasa dakuma Jihar Kano, Mal. Ali Dan Abba.
Da sauransu.
Acikin jawabin Shugaba, yayi addu'o'in alkhairi ga ALH. SUNUSI ABUBAkAR wanda shine ya bayar da kyautar masallacin dakuma makarantar.
Muma muna addu'ar Allah yasakawa wannan bawan Allah dakuma shugabanninmu da alkhairi, Ameen summa Ameen.
Sannan kuma insha Allah MP3 na karatuttukan zasu zo daga baya.
Created at 2015-01-19 07:42:07
Back to posts
UNDER MAINTENANCE
A bit sueripsrd it seems to simple and yet useful.
Kamagra Oral Jelly Berlin buy generic cialis online Buy Cialis Online Canada Viagra Per Impotenza Best Online Pharmacy For Generic Viagra
Buy Doxycycline Online Canada п»їcialis Amoxil 875 For Sinus Infection Amoxicillin And Canine Nursing