Polaroid
Www.awaisuharuna.xtgem.comAwaisu
Maraba da zuwa wannan shafi mai Al-barka

Shafi Don Karuwar Musulmi
Daga Dan uwankuAwaisu Al-Arabee Fagge 2
•Menu•
☀ Home
[«»]Aqidojin Ahlussunnah (100)
[«»]Shi'ah da shi'anci (80)
[«»]Bangarorin Raddi (30)
[«»]Al'amuraan Yau da Kullum (50)
[«»]Rayuwar Musulmi (40)
[«»]Tambaya da Amsa (35)
[«»]Abubuwan Tarihi (75)
[«»]Da'awa Ta Zamani (70)
[«»]Karatu a MP3 (65)
[«»]Vidio (45)
[«»]About me(1)
Wannan shafin mallakarAwaisu Al-Arabee Fagge 3Ne
2025-04-18A'ALAMUS-SUNNAH
س : ما أول ما يجب على العباد ؟
Tambaya ta 1:- menene farkon abinda ya wajaba akan bayi (bayin Allah)?
جـ : أول ما يجب على العباد معرفة الأمر الذي خلقهم الله له ، وأخذ عليهم الميثاق به ، وأرسل به رسله إليهم وأنزل به كتبه عليهم ، ولأجله خلقت الدنيا والآخرة والجنة والنار ، وبه حقت الحاقة ووقعت الواقعة ، وفي شأنه تنصب الموازين وتتطاير الصحف ، وفيه تكون الشقاوة والسعادة ، وعلى حسبه تقسم الأنوار ، ومن لم يجعل الله له نورا فما له من نور .
Amsa:- farkon abinda yake zama wajibi akan bayin Allah shine neman sanin abinda Allah ya haliccesu saboda shi. Kuma yariki alkawari tsakaninshi da bayinsa gameda abin, kuma saboda wannan abin Allah ya aiko da manzanninsa zuwa ga bayinsa, hakannan saboda wannan al'amari ne Allah ya aiko da littattafansa zuwa ga bayinsa, kuma saboda wannan abinne Allah ya halicci duniya da lahira, saboda wannan abin Allah ya halicci wuta da aljannah, saboda wannan abin za'a tashi alkiyama, saboda wannan abin mai afkuwa ta afku, saboda wannan abin Allah ya halicci mizani, kuma saboda wannan abin Allah yasa mala'iku suke rubuta littafi (na aiyukan da mutum yake aikatawa a rayuwarsa), sannan wannan abin shiyake jawowa mutum samun dacewa a lahira ko kuma yayi asara ya tabe. Kuma saboda wannan abin Allah yake raba haskensa ga wanda yaga dama. Duk wanda Allah bai sanya masa haske ba toh babu wani haske da zai iya samu.
Idan mukayi duba ga wannan matsashiyar maganar zamu fahimci cewa dukkannin rayuwarmu tana kewaye da wannan abin da malam yafada mana cewa neman saninsa ne yazama farkon abinda ya wajaba akan kowane bawa daga cikin bayin Allah madaukaki.
Sannan a jimlace zamu fahimci cewa neman ilimi shine abinda yazama dole mutum yafarayi kafin ya shagaltu da aiyukan ibada, domin kuwa dama ibada bata yiwuwa sai an hadata da ilimi. Allah yasa mudace.
س : ما هو ذلك الأمر الذي خلق الله الخلق لأجله ؟
Tambaya ta 2:- toh menene wannan abinda Allah ya halicci halittu saboda shi?
جـ : قال الله تعالى : { وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ }{ مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ } ، وقال تعالى { وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاءَ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا بَاطِلًا ذَلِكَ ظَنُّ الَّذِينَ كَفَرُوا } ، وقال تعالى : { وَخَلَقَ اللَّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ بِالْحَقِّ وَلِتُجْزَى كُلُّ نَفْسٍ بِمَا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ } ، وقال تعالى : { وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ } ، الآيات .
Amsa:- Allah yace "bamu halicci sammai da kassai ba domin kawai arikesu ababan/wuraren wasa, bamu haliccesu (sammai da kassai) ba sai don a tsaida addinin gaskiya acikinsu, amma mafi yawan mutane basu sani ba" Allah yace "bamu halicci sammai da kassai haka kawai ba manufa ba, duk dayake dai wannan shine xaton wadanda suka kafirta" Allah yace "Allah ya halicci sammai da kassai ne domin a tsaida addinin gaskiya acikinsu, sannan kuma idan sun mutu an tashesu ayiwa kowane rai sakamako da irin abinda ya aikata a rayuwarsa ta duniya, kuma hakika Allah bazai zalincesu ba wajen yi musu sakamakon" Allah yace "ban halicci mutum da aljan ba sai de don su bauta min ".
Wannan matashiyar maganar tanuna mana abinda Allah ya halicce mu saboda shi, wannan abin shine bauta wa Allah.
Sannan acikin matsashiyar maganar zamuga cewa akwai sakamako bisa duk ibadarda mutum yayi wa ubangijinsa.
Saide wani hanzari ba guduba! Ita bautar Allah ba yadda akaga dama akeyinta ba, ai da Allah yayi nufin mu bauta masa bai kyale mu haka kawai ba, sai da yaturo mana da 'manual' wato littafinda zamu ga yadda yakeso mu bauta masa, sannan bai kyalemu mubi littafin dakanmu ba saida yaturo mana malaminda zai koya mana abinda yake cikin littafin, wannan malamin shine manzon rahama, farin jakada annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam.
Sannan ita ibada idan anyi ta toh tana bukatar wasu abubuwa guda biyu kafin Allah ya amsheta amatsayin cikakkiyar ibada awajensa wadda zai bada lada akanta. Wadannan abubuwan guda biyu sune:-
1-IKHLASI:- wannan yana nufin idan ka tashi yin ibadarka toh ka tabbata kayi domin Allah shi kadai, baka neman yabon mai yabo, baka damuwa da kushen mai kushe, bakason sakamako daga wajen kowa sai Allah shi kadai.
2-MUTABA'AH:- wannan kuma yana nufin idan ka tshi yin ibadar taka toh ba gaban kanka zakayi ba, zaka tsaya ne kaduba yaya annabi yayi wannan bautar kokuma yaya yace ayi kokuma yaya yaga anayi bai hanaba.
Idan muka hada wannan matashiyar maganar da matashiyar magana ta farko zamu samu wani sakamako wanda zai nuna mana cewa ba'a yin bauta sai da ilimi sannan kuma sai anyi ikhlasi da koyi da manzon rahama sallallahu alaihi wasallam.
Sannan zamuga cewa an halicci dan adam ne domin yaxo duniya yayi bautar mahaliccinsa. Ba kamar yadda wasu suke fadaba suke cewa anhalicci duniya da lahira don manzon Allah SAW, tabbas annabi yanada matsayi da darajar da babu wani mahaluki daya taba samunta kuma babu wanda zai sameta anan gaba. Amma maganar cewa domin shi aka haliccci duniya da lahira wannan ba haka bane, domin acikin bayanin da muka kawo abaya zamu ga wata aya da Allah madaukaki yafadi dalilin dayasa ya halicci duniyarsa da lahirarsa, wannan dalilin kuwa shine domin bayinsa suzo su sami wajen da zasu bauta masa(duniya kenan) ita kuma lahira domin ayiwa bayin sakamakon abinda suka aikata a duniyar. Shikuma annabin an halicce shi ne domin yazo duniya yakowa bayi tadda zasu bautawa mahaliccinsu sannan kuma duk wanda yabishi ya tsira wanda kuma ya kaurace masa ya shiga raminda babu shi ba fita har abadan abada.
س : ما هي العبادة ؟
Tambaya ta 3:- mecece ibada(bauta)?
جـ : العبادة هي اسم جامع لكل ما يحبه الله ويرضاه من الأقوال والأعمال الظاهرة والباطنة والبراءة مما ينافي ذلك ويضاده .
Amsa:- ita kalmar ibada(bauta) suna ne wanda yagame duk wani abinda Allah yakeso kuma ya yarda dashi na aiyuka da maganganu na fili dana boye, sannan da barranta daga duk abinda Allah baya so.
Wannan itace bauta, kenan yanzu duk abinda zakayi sai ka auna shi da wannan ma'aunin domin ka samo masa mahalli.
Fadin cewa duk abinda Allah yakeso kuma ya yarda dashi na aiyuka; ana nufin kamarsu sallah, hajji da sauransu, du wanda da jiki ake yinsu.
Fadin cewa duk abinda Allah yakeso kuma ya yarda dashi na maganganu; ana nufin kamarsu karatun qur'ani, hailala, hamdala, takbirai da sauransu.
س : كم شروط العبادة ؟
Tambaya ta 4:- sharadan ibada nawa ne?

جـ : ثلاثة : الأول صدق العزيمة وهو شرط في وجودها ، والثاني إخلاص النية ، والثالث موافقة الشرع الذي أمر الله تعالى أن لا يدان إلا به ، وهما شرطان في قبولها .
Amsa:- sharuddan bauta uku ne.
1-Gaskatawar gabbai
2-tsarkin niyyah
3-dacewa da shari'ah (qur'ani da hadisi) wadanda Allah bai yarda ayi addinisa ba sai ta hanyar koyarwasu
sukuma wadannan guda biyun na karshe sune sharuddan da aikin yake bukata kafin a amshe shi.
Bayanin wadannan abubuwan zai gudana agaba saboda haka ba sai mun fayyace su ba anan.
س : ما هو صدق العزيمة
Tambaya ta 5:- mai ake nufi da gaskatawar gabbai?
جـ : هو ترك التكاسل والتواني وبذل الجهد في أن يصدق قوله بفعله ، قال الله تعالى : { يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفْعَلُونَ }{ كَبُرَ مَقْتًا عِنْدَ اللَّهِ أَنْ تَقُولُوا مَا لَا تَفْعَلُونَ } .
Amsa:- abinda ake nufi da gaskatawar gabbai shine barin kasala da tawaya wajen bautar, dakuma yin iyaka kokari ta yadda aikin naka zai gaskata furucinka.
Alah yace "yaku wadanda sukayi imani mai yasa kuke fadin abinda baku aikatawa?, ya ishe ku babban laifi awajen Allah indai kuna fadin abinda baku aikatawa".
•fadin cewar aikinka ya gaskata abinda kake fada shine; yadda kake fadin imnai abaki kuma kake fadin musulunci baki bisa so da zabin kanka, toh wajibi ne idann kazo yin ibadar kaji kana yinta ne bisa so ba bisa takurawa ba, ba bisa tilas ba.
ina wadanda idan lokacin sallah yayi suke cewa 'bari muje muyi sallah mu huta/mu sauke nauyi'?
ku tuba ku daina don hakan ba daidai bane.
س : ما معنى إخلاص النية ؟
Tambaya ta 6:- me ake nufi da tsarkin niyyah(ikhlasi)?
جـ : هو أن يكون مراد العبد بجميع أقواله وأعماله الظاهرة والباطنة ابتغاء وجه الله تعالى ، قال الله عز وجل : { وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ } ، وقال تعالى : { وَمَا لِأَحَدٍ عِنْدَهُ مِنْ نِعْمَةٍ تُجْزَى }{ إِلَّا ابْتِغَاءَ وَجْهِ رَبِّهِ الْأَعْلَى } ، وقال تعالى : { إِنَّمَا نُطْعِمُكُمْ لِوَجْهِ اللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنْكُمْ جَزَاءً وَلَا شُكُورًا } ، وقال تعالى : { مَنْ كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الْآخِرَةِ نَزِدْ لَهُ فِي حَرْثِهِ
وَمَنْ كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الدُّنْيَا نُؤْتِهِ مِنْهَا وَمَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِنْ نَصِيبٍ } ، وغيرها من الآيات .
Amsa:- tsarkin niyyah shine bawa ya nufi yardar ubangijinsa bisa dukkanin aiyukansa na magangamu da aiyukansa na fili dana boye.
Allah yace "ba'a umarci(bayi)ba saide domin su bautawa Allah kuma suyi addininsu bisa tsarkin niyya"
Allah yace gameda Abubakar siddiq yayinda yake ciyarda dukiyarsa "baya neman sakamako abindan yakeyi awajen kowa, yanayi ne kawai domin neman yardar ubangijinsa madaukaki"
Allah yafada gameda abinda bayinsa nagari suke fada yayinda suka ciyarda masu karamin hali "lallai mu muna ciyar daku ne kadai don neman yardar Allah, bamuson wani sakamako daga wajenku ko kuma wata godiya"
Allah yace "duk wanda yakeyin aikinsa domin neman sakamako na lahira toh zamu bashi sannan kuma mu kara masa, amma wanda yake aiki domin samun yabo ko lada na duniya toh sai mu bashi a duniyar, amma fa a lahira bashida wani rabo" (akwai ragowar ayoyi da masu yawa dasuke magana akan wannan bangaren )
س : كم مراتب دين الإسلام ؟
Tambaya ta 7:- matakan addinin musulunci guda nawa ne?
جـ : هو ثلاث مراتب : الإسلام والإيمان والإحسان ، وكل واحد منها إذا أطلق شمل الدين كله .
Amsa:- matakan addinin musulunci guda uku ne
1-musulunci
2-imani
3-ihsani
kowannne daga cikin wadannan idan akace za'a fadada shi toh shi kadai ma zai dauki ma'anar addinin.

س : ما معنى الإسلام ؟
Tambaya ta 8:- menene ma'anar musulunci?

جـ : معناه الاستسلام لله بالتوحيد ، والانقياد له بالطاعة ، والخلوص من الشرك ، قال الله تعالى : { وَمَنْ أَحْسَنُ دِينًا مِمَّنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُ لِلَّهِ } ، وقال تعالى : { وَمَنْ يُسْلِمْ وَجْهَهُ إِلَى اللَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى } ، وقال تعالى : { فَإِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ فَلَهُ أَسْلِمُوا وَبَشِّرِ الْمُخْبِتِينَ } .
Amsa:- ma'ana musulunci shine mika wuya ga Allah madaukaki ta hanyarv kadaita shi da bauta, dakuma zurfafawa wajen yi masa makauniyar biyayya, da tsarkaka ga barin hada shi da wani a wajen bauta.
Allah yace "waye yafi kyawun addini fiyeda wanda ya mika wuyansa ga Allah ?"
Allah yace "duk wanda ya mika wuyansa ga Allah kuma yazamanto mai kyautatawa acikin ayyukansa toh hakika yayi riko da igiya mai karfi wadda bata tsinkewa"
Allah yace "kusani cewa ubangijinkiu ubangijine guda daya, ku mika wuya gareshi, sannan yakai ma'aikin Allah kayi bushara(da gidan aljannah) ga wadansa suke kokarin tsarkake niyyoyinsu"

س : ما محل الشهادتين من الدين ؟
Tambaya ta 9:- menene kalmar shahada acikin addini?
جـ : لا يدخل العبد في الدين إلا بهما ، قال الله تعالى : { إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ } ، وقال النبي صلى الله عليه وسلم : « أمرت أن أقاتل الناس حتى يشهدوا أن لا إله إلا الله وأن محمدا عبده ورسوله » " (1) . الحديث ، وغير ذلك كثير .
Amsa:- bawa baya shiga addinin musulunci sai da ita, domin kuwa Allah madaukaki yace "kadai de muminai sune wadanda sukayi imani da Allah da manzonsa

Kuna iya bina ta face book


☀Labarai

KARAIRAYIN ABDULJABBAR NASIRU KABARA

WALLAHI ABDULJABBAR MAKARYACI NE (MP3)
(danna ka saurara kaji inda yafada da kansa )

Yanada kyau mutane masu takamar ilimi yazamanto suna bayyana ka'idojin ilimin a aikace acikin mu'amalarsu da dalibansu, abokanansu malamai dama duk jama'a daga musulmi har arna.

Ga ka'idar ilimi; idan kace babu abu sai wani yace maka akwai a littafi kaza toh kafara zuwa ka duba littafin kafin kace karyane babu.

Abduljabbar ne yayi nufin jinginawa imamul bukhari kin NANA KHADIJAH ta hanyar cewa baiyi mata BABI ba a littafinsa na SAHIHUL BUKHARIY ba, bayan ya fadi hakan sai wani bawan Allah yaje ya duba sai kuma ya gano cewa shi BUKHARIN yayi abinda JABBERIN BAWA yace baiyi ba.

BAYAN AN FADA MASA ANCE MALAM AKWAI WANNAN BABIN FA,

Sai malamin yace "AJE A DUBA, CEWA NAYI BAIYI MATA BABI A KITABUL MANAQIBU BA, IN AKWAI TOH NAYI KARYA, IN KUMA BABU TOH KAMIN KARYA"

Danna kaji inda yafadi hakan da kansa,

http://kiwi6.com/file/457mc1oje2

Toh domin musan JABBERIN karya yakeyi kokuma karya akayi masa sai mukaje muka dauko SAHIHUL BUKHARI.

KWATSAM……… sai ga babi guda BUKHARIN ya ware domin nana khadijah a inda akace baiyi hakan ba.

GA BUKHARI, KUMA GA BABIN, IN ANJE AN DUBA BABU TOH A YAU ZAMUYI RITAYA DAGA IZALA KUMA MUYI RIJISTA A AS-HABUL KAHFI

Abinda bukhari yace:-

كتاب مناقب الأنصار
Acikin kuma yace:
باب تَزْوِيجُ النَّبِىِّ - صلى الله عليه وسلم - خَدِيجَةَ ، وَفَضْلُهَا - رضى الله عنها

3815 - حَدَّثَنِى مُحَمَّدٌ أَخْبَرَنَا عَبْدَةُ عَنْ هِشَامِ بْنِ عُرْوَةَ عَنْ أَبِيهِ قَالَ سَمِعْتُ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ جَعْفَرٍ قَالَ سَمِعْتُ عَلِيًّا - رضى الله عنه - يَقُولُ سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - يَقُولُ حَدَّثَنِى صَدَقَةُ أَخْبَرَنَا عَبْدَةُ عَنْ هِشَامٍ عَنْ أَبِيهِ قَالَ سَمِعْتُ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ جَعْفَرٍ عَنْ عَلِىٍّ - رضى الله عنهم - عَنِ النَّبِىِّ - صلى الله عليه وسلم - قَالَ « خَيْرُ نِسَائِهَا مَرْيَمُ ، وَخَيْرُ نِسَائِهَا خَدِيجَةُ »
3816 - حَدَّثَنَا سَعِيدُ بْنُ عُفَيْرٍ حَدَّثَنَا اللَّيْثُ قَالَ كَتَبَ إِلَىَّ هِشَامٌ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَائِشَةَ - رضى الله عنها - قَالَتْ مَا غِرْتُ عَلَى امْرَأَةٍ لِلنَّبِىِّ - صلى الله عليه وسلم - مَا غِرْتُ عَلَى خَدِيجَةَ ، هَلَكَتْ قَبْلَ أَنْ يَتَزَوَّجَنِى ، لِمَا كُنْتُ أَسْمَعُهُ يَذْكُرُهَا ، وَأَمَرَهُ اللَّهُ أَنْ يُبَشِّرَهَا بِبَيْتٍ مِنْ قَصَبٍ ، وَإِنْ كَانَ لَيَذْبَحُ الشَّاةَ فَيُهْدِى فِى خَلاَئِلِهَا مِنْهَا مَا يَسَعُهُنَّ
3817 - حَدَّثَنَا قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ حَدَّثَنَا حُمَيْدُ بْنُ عَبْدِ الرَّحْمَنِ عَنْ هِشَامِ بْنِ عُرْوَةَ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَائِشَةَ - رضى الله عنها - قَالَتْ مَا غِرْتُ عَلَى امْرَأَةٍ مَا غِرْتُ عَلَى خَدِيجَةَ ، مِنْ كَثْرَةِ ذِكْرِ رَسُولِ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - إِيَّاهَا . قَالَتْ وَتَزَوَّجَنِى بَعْدَهَا بِثَلاَثِ سِنِينَ ، وَأَمَرَهُ رَبُّهُ عَزَّ وَجَلَّ أَوْ جِبْرِيلُ - عَلَيْهِ السَّلاَمُ - أَنْ يُبَشِّرَهَا بِبَيْتٍ فِى الْجَنَّةِ مِنْ قَصَبٍ
3818 - حَدَّثَنِى عُمَرُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ حَسَنٍ حَدَّثَنَا أَبِى حَدَّثَنَا حَفْصٌ عَنْ هِشَامٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَائِشَةَ - رضى الله عنها - قَالَتْ مَا غِرْتُ عَلَى أَحَدٍ مِنْ نِسَاءِ النَّبِىِّ - صلى الله عليه وسلم - مَا غِرْتُ عَلَى خَدِيجَةَ ، وَمَا رَأَيْتُهَا ، وَلَكِنْ كَانَ النَّبِىُّ - صلى الله عليه وسلم - يُكْثِرُ ذِكْرَهَا ، وَرُبَّمَا ذَبَحَ الشَّاةَ ، ثُمَّ يُقَطِّعُهَا أَعْضَاءً ، ثُمَّ يَبْعَثُهَا فِى صَدَائِقِ خَدِيجَةَ ، فَرُبَّمَا قُلْتُ لَهُ كَأَنَّهُ لَمْ يَكُنْ فِى الدُّنْيَا امْرَأَةٌ إِلاَّ خَدِيجَةُ . فَيَقُولُ إِنَّهَا كَانَتْ وَكَانَتْ ، وَكَانَ لِى مِنْهَا وَلَدٌ
3819 - حَدَّثَنَا مُسَدَّدٌ حَدَّثَنَا يَحْيَى عَنْ إِسْمَاعِيلَ قَالَ قُلْتُ لِعَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِى أَوْفَى - رضى الله عنهما - بَشَّرَ النَّبِىُّ - صلى الله عليه وسلم - خَدِيجَةَ قَالَ نَعَمْ بِبَيْتٍ مِنْ قَصَبٍ ، لاَ صَخَبَ فِيهِ وَلاَ نَصَبَ
3820 - حَدَّثَنَا قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ فُضَيْلٍ عَنْ عُمَارَةَ عَنْ أَبِى زُرْعَةَ عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ - رضى الله عنه - قَالَ أَتَى جِبْرِيلُ النَّبِىَّ - صلى الله عليه وسلم - فَقَالَ يَا رَسُولَ اللَّهِ هَذِهِ خَدِيجَةُ قَدْ أَتَتْ مَعَهَا إِنَاءٌ فِيهِ إِدَامٌ أَوْ طَعَامٌ أَوْ شَرَابٌ ، فَإِذَا هِىَ أَتَتْكَ فَاقْرَأْ عَلَيْهَا السَّلاَمَ مِنْ رَبِّهَا وَمِنِّى ، وَبَشِّرْهَا بِبَيْتٍ فِى الْجَنَّةِ مِنْ قَصَبٍ ، لاَ صَخَبَ فِيهِ وَلاَ نَصَبَ
3821 - وَقَالَ إِسْمَاعِيلُ بْنُ خَلِيلٍ أَخْبَرَنَا عَلِىُّ بْنُ مُسْهِرٍ عَنْ هِشَامٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَائِشَةَ - رضى الله عنها - قَالَتِ اسْتَأْذَنَتْ هَالَةُ بِنْتُ خُوَيْلِدٍ أُخْتُ خَدِيجَةَ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - ، فَعَرَفَ اسْتِئْذَانَ خَدِيجَةَ فَارْتَاعَ لِذَلِكَ ، فَقَالَ « اللَّهُمَّ هَالَةَ » . قَالَتْ فَغِرْتُ فَقُلْتُ مَا تَذْكُرُ مِنْ عَجُوزٍ مِنْ عَجَائِزِ قُرَيْشٍ ، حَمْرَاءِ الشِّدْقَيْنِ ، هَلَكَتْ فِى الدَّهْرِ ، قَدْ ، أَبْدَلَكَ اللَّهُ خَيْرًا مِنْهَا

LAAAAAAAAAAAAAA MALAM YA KWANTARA KARYA

Amma fa kada kuga laifi na don nace yayi karya, domin shine yace idan akwai yayi karya, in kuma babu anyi masa karya, toh kuma gashi mun samu, toh yaya kenan??????

AMMA ANJI KUNYA WALLAHI

Ace duk kurin ilimin da akeyi ashe ko bukhari ba'a wuce ba??????

Wani mai waqa yayi gaskiya, kunsan mai yace????

فآر ثم آر ثم آر
شقاق المرء من أجل الطعم
Allah yasa dai mabiyan suna fahimtar mai ake cewa.

Awaisu Al'arabee Fagge
20-1-2015

Back to posts
Comments:
[2015-04-22 21:03:29] sai baba buhari :

yayi daliban na shine kawai basa karatu kuma suna binshi a makance

[2015-04-30 20:56:43] Bashir Ummar :

Yan Izala Bakuda Kunya Akwai Makaryarta Kamarku

[2015-05-21 13:56:41] mark2245 :
[2015-06-18 20:46:42] MANDE :

DON ALLAH awaisu A wane cassete ne abduljabar yace sai yakashe SHK JAFAR

[2015-09-09 10:41:14] Abubakar Ibraheem khaleel :

kai uwaisu al'arabee kaji tsoron Allah malam cewa yayi bukhari bai yi mata babi ba a manaqibu kuma haka ne, amma kai kazo kana wata irin magana kaji tsoron Allah.....! malam ikon Allah wllh ya sha gabanku...... sai dai kuyi haquri

[2015-09-09 10:53:33] abubakar ibraheem khaleel :

kuma ai sai dai ku dinga bata wa mutum suna alamun an fi qarfinku. ku kawo amsoshin littafin da m.sarki ya rurrubuta, to anan ne za mu gane cewa salafiyya ta haifu..... duk kun bazama kun haukace kun dimauce saboda mutum daya kawai Shugaban 'yan kogo.

[2015-11-12 19:23:39] Basheer Adamu Khadeer Aliero :

Wannan ba addini ba ne mu dinga neman laifin wani domin mu fallasa shi idan kai mai tunani ya kamata ka maganarsa da yayi ta gaskiya ka yadawa jama'a domin na tabbata gaskiya tafi karya.

[2016-04-02 15:43:29] Abubakar sagagi :

Kuda. Yahudawa du dayanai. Mutanan. Kawai. Yan. Izalar. Karya

[2016-04-13 14:38:38] IDRIS DAHIRU :

kai awaisu.musan bukarinfa kada kada hankalin jahilai mana

[2016-04-21 05:40:43] Muhammad Kabir Ingawa :

Kai Mai da'awar al-Araby a Ina ka samo wannan suna? To Ina Mai fada maka cewa Mal. Abduljabbar a duniyar Wahabiyya Kaf wallahil azeem basu da Tamkar farcensa. Kuma iyayen gidanka basu iya tararsa ba balle Kai da yayi Jika da Kai. Shawara Zandam Baka kaje kayi karatu ya fiye maka wadannan zage-Zagen. Ina tabbtar maka da cewa Mal. Ya girmi duk ire-Irene wannan hauragiyar. Wassalamu ala manittabaal huda.

[2016-06-11 10:20:21] Abdulgaffar kalgo :

kai jahilin muridin Abdul jabbaru abubakar sagagi ka yi hattara

[2016-07-09 04:32:45] XPFU8YQpWm :

Home run! Great slnugigg with that answer!

[2016-07-07 10:43:10] muhammad kabir :

kai yaro ka koma makaranta bakwa game karatu ancebaka babu babi guda data warewa Nana khadija wannan babin yana magana kan Qur'an Nana khadija kuma aciki aiyakawo maganar Nana maryam kaga kenan ba Nana khajija kawai ake maganaba itaka dai adinfa karatu Dan Allah

[2016-08-16 23:10:13] muhammad garba amin k/na'isa :

yan wahabiyya Allah ya ganar daku inzaku gane gaskiya inkuma bazaku gane ba Allah yai mana maganin ku

[2016-08-30 20:01:00] ISYAKU ISAH RIMI :

ALLAH YA KARAMANA SAN MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM DAN ALLAH YAN IZALA ADAINA KIRKIRAR KARYA BA KYAU.

[2016-09-20 00:06:24] SON ANNABI DOLE :

Da mutanenku da aljanunku, manyanku da yaranku, mazanku da matanku, rayayyunku da matattanku dukkanku bazaku iya da ABDULJABAR ba gwanda ma kubar bata wa kanku lokaci

[2016-10-07 21:11:16] Bashir auwal al-funtawy :

Salam.
Bekamata mu rudu da kuskuren wani malami ba dan ba ya aqidar mu, domin kuskure alama ce da take numa dan adanci.

[2016-10-12 12:46:02] قريب الله علي :

I dan ana neman baban maƙaryaci aka sami ibini taimiya to ashafa fatiha,har annabi(S.W.A)Yiwa karyar yake

[2016-11-13 21:18:34] ابو عبد الرحيم :

اللهم يبارك

[2016-12-12 23:16:45] MATASHI :

Allah ka bawa shehin samarin kogo turmin gaskiya ya casa izala da salafiyya


UNDER MAINTENANCE




•Home•


«Kuna iya bina ta face book»

«Ko ta shafin mu na Tsarabar sunnah»

«Ku ziyarci Shafin Basheer journalist sharfadi»





  • AWAISUL-ARABEE FAGGE
  • ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow